MANYAN WAYOYI BIYAR MASU ARAHA A NIGERIA DA SUKE AIKI DA 5G NETWORK
duba da yadda harkar fasaha da kerakere take kara bunkasa a fadin duniya A yau, Mun samu gata da kuma damar yin dayawan ayyukanmu da suka shafi harkar na'ura cikin sauri da kuma sauki. Koda yaushe ilmin fasaha da kera kere kara bunkasa yake musamman a Bangaren Na'ura Mai kwakwalwa wato Computer da kuma Na'ura ta wayoyin sadarwa.
Shekaru kadan da suka wuce muna samun damar shiga yanar gizo ta Bangaren cibiyoyin sadarwa daban daban kamar tsarin 2G (EDGE) Wanda ke bamu damar shiga yanar saide yanada matukar jinkiri, sai kuma 3G Wanda shima din de baida saurin saide yafi 2G, saikuma 4G Wanda shine mukafi Aminta dashi domin yana biya mana buqatu ne cikin gaggawa a mafi yawancin wayoyinmu, to kamar de haka ansamar da tsarin 5G kwanan nan, da 5G ne mutane da yawa zasu samu damar shiga internet cikin sauki da kuma biyan buqata cikin gaggawa sannan shi dama tsarin na 5G akwaeshi a wasu wayoyinmu da muke Amfani dasu a nan kasar Nigeria saide Babbar kalubalan da muke fuskanta itace har yau bamuda tsarin 5G a Nigeria Amma meyasa muke sayen wayoyin da sukeda 5GB network? Albishirinku An gwada tsarin 5G kuma kwanan nan za'a samar dasu a wasu jihohin dake kasar nan saboda haka duk wadda yake da wayar 5G kamar garabasa zata zame masa.
Kada ka manta dayawa daga cikin wayoyin nan suna nan a shagunan wayoyi na Nigeria, abun tambayar anan shine, shin sunyi dede da ra'ayinka ko kuwa suna daga jerin wayoyin da kakeso?
Karka damu zamu bayyana muku Biyar daga Cikinsu a kasa wadda sukeda saukin farashi a kasar nan anan zaku nemi duk kalar wayar da kukeso.
Dafari Mene ne 5G Network?
5G Network shine karni na Biyar na wireless Technology wadda yake da fiko wajen sauri a Bangaren Internet da kuma karancin aibu, 5G network yafi 4G LTE a Bangare da dama sannan yakan baka damar shiga internet cikin sauri, da download file quicker, saukar da manyan Videos a Lag mafi kasa, da kuma buga games ta online ba slow.
Zuwa yanxu nasan kun fahimci kadan daga tsarin 5G bari muyi abunda ya kawomu zamu shelanta muku wayoyin da suke kan tsarin 5G da kuma farashinsu.
5 dasukafi sauki a kasarmu sune, Akwae:
1. Samsung Galaxy A22 5G:
Samsung sun fitar dawayar nan ne a shekarar data gabata, kuma ta Kasance a cikin wayoyin da sukafi girma akamfaninsu, sannan tafi kowacce saukin kudi, wayar tana daukan 5G network kuma tana temakawa masu Amfani da ita wajen shiga yanar gizo ta cikin hanzari a Bangaren 5G network, sannan tanada memory na kanta 6GB storage space nata kuwa yana kaiwa 128GB with android 11 processor, Battery ta kuwa yanada girman dayakai 500mAh, Operation system nata shine Android Os 11 abun mamaki dukda wannan kaya datake dasu kudinta Baya wuce naira dubu dari da uku #103,000
2. Tecno pova 5G:
Wannan ma tana daga cikin wayoyin da zaka iya mallaka a matsayinka na Wanda yake harka online kullum, domin kuwa tanada matukar karfin shiga Internet ba gargada ga sauki da dadin Aiki tanada battery Mai mega 6000mAh sannan Camera ta guda uku ce Mai karfin 50MP, tana zuwa da storage me Nauyin 128.GB ROM da kuma 8.GB RAM, android processor 11 ta samu karbuwa wajen HIOS 8.0 don tabbatar da ingancinta
3. Redmi Note 10:
Wannan kamfanin yakai tsawon shekaru 3 a Nigeria, wadda dukkanmu Mun yarda cewa kamfanin wayoyi na Xiaomi suna daga cikin kamfanin da sukafi kirkirar kyawawan Na'urori na karin fasahar wayoyin zamani a duk fadin kasuwar wayoyi ta duniya, wayar Redmi an fitarta ne a watan June na shekarar 2021 sannan tana aiki da 5G network ne kuma tanada saukin aiki wajen Bangaren tracking da harkar data shafi hacking, wayar tanada 4G RAM sannan tanada model guda biyu ne 64GB da kuma 128GB sai wadda ka zaba Battery ta yakai 5000mAh capacity, Operation system: Android 11 Os, MIUI 12 kudinta kuwa Baya wuce dubu tamanin da daya da dari biyu #81,200
4. Oppo A74:
Wannan ma tana daga cikin manyan wayoyin da zaka iya mallaka masu aiki da 5G Anyi launched dinta ne a 31 ga watan August 2021, wayar Oppo tana aiki ne da operation system na Android 11 Os sannan tanada battery Mai karfin 5000mAh memory ta na ciki da kuma na kanta sunkai 6GB RAM da kuma 128GB ROM zaka iya saukar da kowanne kalan application akan RAM dinta batada matsala
5. Infinix Zero:
Har gobe kamfanin infinix basu kirkiri wayar da takeda power a Bangaren 5G network ba kamar Infinix Zero, sun fitar ta ne a watan february na shekarar 2022. Tanada battery Mai karfin 5000mAh battery ta ya mynada karfin gaske, Os 11 processor tabbaci daga kamfanin Xos 10 sannan itama kudinta Baya wuce naira dubu dari da goma sha shida kacal #116,000.
Dan uwa kasani 5G network duniya ne zai baka damar shige da fice a Bangaren Internet saboda bashida da wàni aibu a Bangaren jinkiri, daga yau kallon film a network ba matsalar ka bace saide wàni uzuri na daban, sannan zaka iya saukar da dukkan wàni file na Android cikin sauki bakada matsalar a tsarin 5G, duk da cewa yanada Jan data dayawa to amma de kam ya kawar ma da ciwon kan ka dan haka ma kuda yake cewa wajen biyan buqata Rai ba a bakin komai yake ba to dai muna marabtarku da sabon tsarin da zai shigo mana Nigeria.






0 Comments