Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

HANYOYI SHIDA DA SUKESA SOYAIYA BATA TSUFA HAR MUTUWA

 


Hanyoyi Shida da zasu dauwamar da Rayuwar Aurenku cikin yarda da soyaiya..!

Sauda dama mutane sukan cewa da zarar Anyi Aure an haihu shikenan ba sauran soyaiya ba Nuna damuwa da kewan juna, wadda ko shakka babu wannan kuskure ne da ma'aurata sukeyi musamman na wannan zamanin,

Wannan kuskuren kuwa yana daga cikin ababen da suke kawo rabuwan Aure ko kuma Rashin zaman lafiya a gidajen ma'aurata!

Todae kamar yadda na fada zan kawo muku abubuwa guda Shida wadda a kalla idan muka rikesu zamuci Ribar Aure kuma ina kyautata zaton zamu dade cikin shaukin soyaiya da kaunar juna koda kuwa ace tsufa ya riskemu

Abu na farko anan shine:

1. Soyaiya da shakuwa: ko shakka babu soyaiya tana taka rawar ganin wajen dorewar Aure wadda asalinta tana samuwa ne tun kafin Auren kuma saida itane Aurenma yake Amsa sunansa, domin kuwa duk soyaiyar da kukayi a waje matukar bakuyi Aure ba to kamar kunsha shayi ne ba sugar Saboda duk dadin lnuwar gemu batakai ga makogwaro ba.

2. Jima'i: wannan Kam kusan ma itace dalilin Auren idan Mun fahimta zamuga ko a Addu'ar ma'aurata abunda ake cewa shine Allah ya bada zaman lafiya ya kuma kawo kazantar daki saide muna shagalta da halin saduwa da kawae Mun dauka biyan bukatar lokaci guda shikenan an wuce wajen A'ah yana dakyau mu nemi Ilmi gameda saduwar ita kanta Akawe kalolin kwanciya da iyali daban daban wadda suka halatta ko a Addini babu laifi mu nemesu don muna morewa lokacinmu na wannan yanayin sannan musamman Mata yana dakyau kuna Amfani da magungunan da suke kara muku Ni'ima don kara burge mazajenku a duk sa'adda suka sadu daku hakan zai kara dauwamar da Aurenku sosae dagaske!

3. Aminci da gaskiya: Aduk sa'adda ka Auri mace yakamata kasan cewa Amanace aka baka kada kayi kokarin Tauye Mata hakki ta kowacce Hanya, sau dayawa zakaga duk Mutumin da yayi Aure samunsa yana karuwa ne sosae don Allah ne yake sanyawa nemansa Albarka, alokacin da kana tuzuru Allah yana baka kasonka ne nakai kade amma da zarar kayi Aure saiya hadama Dana Matarka donka killaceta a gida tabar gidansu ta dawo wuyanka don haka kada kaji kyashin kashe Mata matukar ba almubazzaranci bane, kema haka yana dakyau kiyi riko da amana banda rage kudin cefane da caje aljihu da kuma baza sirrin miji a anguwa da gidajen Yan uwa domin wannan duk yana karkashin Amana ne.

4. Hakuri da juna: Masana iya magana cikin hikima sukace ita mace kamar sabuwar kwarya ce, ina ma'anar wannan maganar take? Ka duba kwarya lokacin tana sabunta idan aka zuba ruwa a ciki zakaji Ruwan ba dadi daci ne kawae idanma baka rintse ido ba bazaka iya sha ba, amma a kwana a tashi inde ana Amfani da wannan kwaryar za a wayi gari idan aka zuba ruwa zakaji har wàni zaki zaki yake, saboda haka hakuri shine matakin nasara a Karo na farko kuma dole sai kuna Hakurin kafin kuci Ribar zamantakewa.

5. Yafiya: Bahaushe yace zomu zauna tamkar zomu sabane, Amma mezai shiryar daku idan kun saba itace Yafiya! Shakka babu Neman yafiyar juna ita zata dawo daku hanya aduk sanda kuka kauce Amma saikun cire girman kai kuna rokon gafarar junanku.

6. Kulawa da Juna: kana gida ko office koma a duk wàni wajen sana'arka ace ka sabarwa Matarka da Kira ko Sakonnin Soyaiya ta yadda zata fahimci yadda kake jinta a ranka matukar kunayin hakan to ko baka kusa za'a Kasance ana kewanka kuma ana jiran dawowarka sannan, kema in kina yiwa mijinki hakan to bazaiji sha'awar kula yan matan waje ba kema kuma shedan bazai tunxuraki kinemi wasu mazan ba ko a gida koma a kafafen sada zumunta facebook, whatsapp da sauransu.

Na takaita Biyar ne domin sune jigon, ko shakka babu wadda duk suka rike wadannan sun shirya tsaf domin ganin sun dauwamar da Aurensu Allah kuma zai dafa musu bazai bari shedan yaci galaba a kansu ba.

Nagode kuyi following namu a page dinmu domin samun gamsassun Bayanai wadanda suka shafi Al'amuran yau da kullum Musamman ma a bangaren ku Masoya domin kune jigon Rayuwan 

Shugaba

Post a Comment

0 Comments