Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

AN GANO TSUNTSUWAR DA TAFI JIRGI GUDU



AN GANO TSUNTSUWAR DA TAFI JIRGI GUDU

Masana iya magana sukace abun al'ajabi Baya karewa, Hakika yau mun taho muku da labari na wata tsuntsuwa Mai ban mamaki wadda tayi tafiyar kilometers 12112km batare da ta huta ko ta tsaya cin abinci ba, wannan tsuntsuwa Mai suna godwit tana cikin jerin tsintsayen da sukeda tsayi da kuma dogun kafafu sannan tana jerin tsuntsaye masu doguwar tafiya a sararin samaniya bugu da Kari tsuntsuwar tana jerin tsuntsayen da suke doguwar tafiya a cikin ruwa har sukan canza sheqa daga wannan yankin su koma wàni daban, dangin tsuntsayen ce nau'ikan Limosa, Nisan tafiyar da take aban kasa yakan temakamata wajen samun abinci kamar tsutsa da kuma dodon gori da makamantansu amma da zarar lokacin hunturu yayi sukan tashi ne rukuni guda suyi kaura zuwa Lardin da abinci zai wadacesu sannan su yada zangonsu a nan, tsuntsuwar tana Rayuwa ne Yankunan teku da kuma tsibiri sannan da rani tana zaka ne a Arewacin teku idan damina tayi kuma saita canza sheqa zuwa kudanci, macen tsuntsuwar wadda takeda doguwar jela tana iyayin gudu kilometers dubu ashirin da tara 29,000km wadda tayi dede da 18,000mi, batare da ta huta ba Sannan tana tashi sararin samaniya tsawon kilometers dubu goma sha daya da dari shida da tamanin 11680km wadda yayi dede da 7260mi batare data huta kotaci abinci ko shan ruwa ba, A shekarar dubu biyu da ashirin dede tashar Avian ta non stop flight sake Alaska ta Birnin Amurka ta dauki bayanan tsuntsuwar Inda ta sanya tracker a kafarta don gano adadin gudunta a sararin samaniya, sun gano tsuntsuwar tayi gudun kilometers dubu goma sha biyu da dari biyu 12,200km wadda yayi dede da 7600mi batare data tsaya ba, Inda ta fara tafiyan tun daga Alaska na kasar Amurka har zuwa Birnin New Zealand na Kasar Australia wato nisan a kalla yakai jirgi ya tashi daga Nigeria yaje saudiya ya dawo sau hudu, kaga ita kuwa aiko a gantali dadi zataje Saudi ta dawo,, Allahu Akbar ko shakka babu wannan tsuntsuwar tanada abun al'ajabi domin har zuwa yau ba a taba kirkirar wani Kayan sanfuri dayakaita tafiya ba, domin ko jirgi yayi wannan sufurin dole zai buqaci hutu balle wata mota ko Babur.



Post a Comment

0 Comments