Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

KO KASAN MIKIYA TAKAN IYA SHEKARU 70 A DUNIYA?

 


KO KASAN MIKIYA TAKAN IYA  SHEKARU 70 A DUNIYA?

Ko shakka babu mikiyi tanada Alfarmar tsawon Rayuwa a a duniya harna tsawon shekaru 70 wannan wata baiwa ce daga cikin baiwar da Allah ya Mata a rayuwarta, saide kuma ba kowacce bace daga Cikinsu take iya jurar yanayin da zata shiga kafin tayi wadannan shekarun a duniya, mafi yawancinsu sukan hakura da Rayuwar ne tun suna Yan shekara Arba'in a lokacin da tsufan farko ya cimmusu domin kuwa duk wadda takeson ta kara shekara talatin a rayuwarta dole ne saita dauki wàni mataki wadda yakan basu wahala kwarae dagaske!

A lokacin da mikiya takai shekaru 40 a duniya a dede wannan lokacin tsufa ya cimmata kaifin faracenta sun disashe gashinta ya tsufa ya Mata Nauyi bakinta ba kaifi ko kadan a dede wannan lokacin ne abinci yake gagararta domin batada kaifin farce duk abunda ta kama kwacewa yake, a dede lokacin nan ne yunwa take Addabar ta saiya zama dama biyu ne ya rage mata a duniya kode ta hakura ta mutu ko kuma tazabi ta canzawa kanta Rayuwa!

Ga yadda takeyi domin komawa sabuwar rayuwa:

Dafarko zata ware kwanaki 150 wato kimanin watanni Biyar kenan cikin rayuwarta sannan dole ta kauracewa Rayuwa a cikin dabbobi yan uwanta domin gudun kada su halakata zata koma can sama ta nemi wàni tsauni mai nisan gaske ta boye cikinsa wadda babu wata dabba da zata kusanceta harta gama jinyarta, abunda take farayi a jikinta shine zata wasa bakinta ne har sai yayi kaifi sannan ta cire faracenta tajira har sai wàni sabo ya fito sannan daga nan zata fara fizge gashinta yana jini a haka zatayi ta fizgewa harsai ta cireshi gaba daya sannan ta zauna zaman jinya har saita warke gaba daya daga nan kuma idan tagama zata fito a matsayinta na sabuwa zata karbi kambunta na King on Birds daga nan ne zata iya kara shekaru Talatin a rayuwarta na gaba..!

Meyasa mikiya ta buqaci ta gyara kanta?

Saboda ta tsira ta kuma sake sabuwar Rayuwa.! Mu kanmu munada buqatar canji donmu gyara Rayuwarmu meyasa bazamuyi ba? Kowannenmu yanada muggan dabi'u halaye marasa kyau amma mun kasa canzawa, inde har mikiya takan iya canza rayuwarta tanada shekaru 40 mu meyasa bazamu iya canza Namu ba?  Babu shakka akwae buqatar mu wanke zuciyoyinmu mu gyara dabi'un mu kamar mikiya donmu mori sauran lokacin da suka rage mana. 

kokunsan cewa A duk lokacin da ana Ruwan Sama Tsuntsaye Suna neman mafaka ne? Amma ita mikiya batada buqatar wajen buya saidema tayi sama ta tafi can sararin samaniya cikin gajimare ta morewa lokacinta saboda haka mu fahimta cewar matsalolinmu sunada magunguna da dama bawae masalaha daya zamu nema ba,

Ina fatar wannan Tarihi na mikiya zai zama Silan canzawar wasu daga cikinmu saide hakan bazai yiwu ba saimun temaka wajen yada wannan Tarihi don yan uwanmu su fa'idantu da wannan ina fatar za'a mana Share.


Post a Comment

0 Comments