AMBALIYAR RUWA TA KASHE MUTANE 19 A YAMEN
A safiyar yau Juma'ah 12/August/2022 ne dai mutanen Birnin SAN''Äa na kasar Yamen suka tashi da gagarumar Ambaliyar Ruwan Sama mai dauke da iska, tsawa da kuma cida wadda a kalla Ruwan yayi kimanin kwanaki uku zuwa hudu yana sauka daga sama, Ruwan yayi sanadiyar mutuwar mutane goma sha tara 19 ya kuma raunata a kalla mutane sama da Ashirin inji mazauna Birnin, Majiyar labaran ta CGTN ta zanta da wàni dattijo Mai suna Muhammad Badvi donji ta bakinsa, dattijon yace tun yarintarsa yake zaune a Birnin SAN''Äa amma rabon dayaga Ruwan Sama Mai yawa irin wannan tun shekarar Alif dubu daya da dari tara da saba'in shima kuma wancan da akayi na bayan baikai wannan yawa da kuma ta'adi ba.
Daga bangaren Masana alkaluman kasar kuwa sunce tun a tsakiyar watan July suka shiga cikin yanayi na Marka Marka wadda zuwa yanxu daminar tayi ajalin mutane sama da 84 dalilin Ambaliyar dake gudana a cikin kasar.
0 Comments